Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato rahoto daga shafin sadarwa na jaridar Al-qbas ta kasar Kuwait cewa, kasashen da suke gudanar da taruka domin kawar da Mu’ammar gaddafi na kasar Libya sun kudiri aniyar ci gaba da gudanar da taruka domin makomar kasar bayan kawar da Gaddafi wanda kasashen yammacin turai suka kawar da shi.
Wadannan ayoyi biyu suna magana ne kan wadanda suke boye abin da suka sani na daga abin da Allah ya safkar a cikin littafinsa, inda ayoyin ke yin nuni da cewa hakan fadawa ne a cikin fushin ubangiji da azabarsa. Ilimi shi karon kansa ba shi ne kadai ba ne hanyar sa’ada, matukar ba a yi aiki da shi ba, bil hasali ma ma’abucinsa zai iya zama cikin bata fiye da jahili, a lokacin ya yi amfani da shi wajen boye gaskiya da karkatar da mutane zuwa ga wani abun da Allah bai yarda da shi ba.
Al’ummar musulmi tana cikaken bayani daga al’ummomin da suka gabata, a lokacin da masansu suke boye ilimi tare da batar da mabiyansu, da rashin yin umurni da kyakkyawa, da kuma rashin yin hani daga mummuna.
850920