Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, A zahiri lamri yake cewa irin wannan imani na bukatar a gan shi a aikace a cikin ayyukan ibada, kamar su salla, kyautata ma masu rauni da taimakon mubukata, ciyarwa saboda Allah, bayar da zakka da dai sauran ayyuka makamantan hakan.
Samun kusanci da Allah ba shi ne abin da ake bukata ba kawai, babban abin da ake bukata shi ne samun kusanci tare da kiyaye shi, wato ba aikata aikin da zai kusantar da mutum zuwa ga Allah ba, a wani lokaci kuma mutum ya aikata abin da zai nisantar da shi daga Allah, tare da rusa ayyuaknsa na alkhairi.
Samun tabbatuwa kan kusanci ga Allah yana kasancewa ne ta hanyar kiyaye kyawawan dabi'u, hakuri, cika alkawali, kiyaye hanin Allah, da aikata umurninsa, da sauran abubuwa makamantan hakan, su ne suke taimaka ma mutum wajen tabbatuwa kan kusanci ga Allah madaukakin sarki a kowane lokaci.
Wannan ayar tana nuna mana cewa mumini shi ne wanda yake bayar da hakkin Allah daga duniyarsa wanda ya wajabta masa wato zakka, da kuma abin da ma ba a wajabta masa na daga ciyarwa daga dukiyarsa domin Allah.
850889