Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na saphirnews an bayyana cewa, mafi yawan musulmi da suke zaune a kasashen yammacin turai za su yi idin karamar sallah a yaua talata bisa fatawoyin da malamai daban-daban suka bayar kan hakan inda da dama daga cikin kasashen musulmi ma a yau ne suka yin wannan sallah mai albarka.
A labarin da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an sheda cewa, mafi yawan kasashen musulmi sun sanar da ranar yau talata a matsayin ranar idin karamar salla, inda ake ta gudanar da shagulgula da murna da kuma annashawa da hakan ya hada har da wasu daga cikin yammacin trai kamar dai yadda rahoton ya tabbatar.
Musulmi da suke zaune a kasashen yammacin turai za su yi idin karamar sallah a yaua talata bisa fatawoyin da malamai daban-daban suka bayar kan hakan bisa dogaro da dalilansu na shari'a wadanda ake lissafin wata da su.
851868