Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa kungiyar 'yan tawayen kasar Libya ta samu kujera a majalisar kungiyar hadin kan kasashen larabawa a matsayin mai wakiltar kasar a hukumance kamar dai yadda bayanai suka tabbatar da hakan daga majiyoyin kungiyar ta hadin kan kasashan larabawa a jiya.
Mayakan juyin juha halin Libya sun yantar da mutane 10,000 daga cikin fursunonin siyasa sama da 50,000 da Muammar Gaddafi ya tsare a gidajen kurkuku.,akakin sojojin juyin juya hali Ahmed Umar Bani ya bayyana damuwa matuka a kan yanayin da sauran dubban fursunonin suke ciki wadanda ma ba a san inda suke ba.
Kakakin ya kuma bukaci duk wanda ya ke da labarin inda fursunonin suke tsare ya fada wa hukuma, ya kuma ce duk wanda boye wani labari dangane da hakan za a dauki shi tamkar yana da hannu a wadannan laifuka.
Ahmed bani ya ce ana gano manyan kaburburan da aka bisne mutane a kewayen gine-ginen da ake tsare mutane da gidan kurkukun Abu Salim wanda ya yi kaurin suna, kasar Libya dai ta fara fuskantar ayyukan tashin hankali ne tun a cikin watan janairun farkon shekarar nan.
851598