IQNA

Bude Reshen Bankin Musulunci A Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa

12:57 - August 31, 2011
Lambar Labari: 2179752
Bangaren kasa da kasa, a karon farko za a bude bangaren yin nazari a kan harkokin bankin muslunci da yake kula da ayyuka na musamman ta fuskacin harkokin kasuwanci a jami’ar CUD da ke birnin Dubai cibiyar kasuwanci ta hadaddiyar daular larabawa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadrawa na yanar gizo na bi-me an bayyana cewa, a karon farko za a bude bangaren yin nazari a kan harkokin bankin muslunci da yake kula da ayyuka na musamman ta fuskacin harkokin kasuwanci a jami’ar CUD da ke birnin Dubai cibiyar kasuwanci ta hadaddiyar daular larabawa a cikin ‘yan watanni masu zuwa.
A mafi yawan lokuta kalma guda ta kumshi wasu haruffa ne wadanda idan aka hada su suke tayar da wannan kalmar da kuma bat a ma'ana. Amma Allah Madaukakin Sarki ya faro wasu surori 29 cikin surori 114 da Alkur'ani mai girma ne da wasu haruffa wadanda kowane guda daga cikin su ana karanto shi ne shi kadai dinsa. Misalin hakan ita ce wannan aya ta farko ta cikin Suratul Bakara wanda muke karanta wa A L M ba wai Alam ba kamar yadda ya kamata su kasance. Irin wadannan haruffa wadanda larabawa ma ba su saba da su ba masana Alkur'ani suna kiran su da sunan 'huruf al-Mukadda'a' wato haruffa da suke rarrabe da junansu wadanda kuma a rarraben ake karanta su.
A mafi yawan lokuta bayan wadannan haruffan, akan gabatar da aya ta gaba ne wacce za ta yi nuni da girmar Alkur'ani da kuma kasantuwarsa a matsayin wata mu'ujiza, kamar yadda ya zo cikin Suratush Shura 'Ha mim Ain Sin Kaf daga nan sai ya ci gaba da cewa: "Haka nan kuma sai ya yi maka wahayi da kuma wadanda suka zo a gabaninka, lalle Allah mai girma ne kuma mai hikima".
Tamkar Allah Madaukakin Sarki yana son ya ce ne ni dai na samar da wannan littafi na wa ne wanda kuma yake a matsayin mu'ujiza daga wadannan haruffa da kuka riga da kuka san su ne, ba wai daga kalmomin da ku din nan ba ku san su ba ne ko kuma ba za ku iya fahimtar su ba.
852470
captcha