IQNA

Ana Tarukan Idi A Mafi Yawan Kasashen Musulmi Na Duniya

12:47 - August 31, 2011
Lambar Labari: 2179758
Bangaren kasa da kasa, a mafi yawan kasashen musulmi na duniya an gudanar da bukukun idin karamar salla ne a jiya talata, duk kuwa da cewa a wasu kasashen musamman jamhuriyar musulunci da Iraki duk a yau ne suke gunar da na su tarukan.
Kamfanin dilalncin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da yanakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, mafi yawan kasashen musulmi na duniya an gudanar da bukukun idin karamar salla ne a jiya talata, duk kuwa da cewa a wasu kasashen musamman jamhuriyar musulunci da Iraki duk a yau ne suke gunar da na su tarukan na idin karamar salla na wannan shekara.
Bisa la’akari da cewa an zabi birnin Najaf mai alfarma daga bangaren cibiyar raya al’adu da ilimin musulunci ta duniya a matsayin birnin al’adun musulunci na shekara ta, cibiyar adana ayyukan bincike kan kur’ani mai tsarki ta Alil Bait (AS) na da shirin gudanar da wani taro, da za a zabi shiri ko bincike da ya fi kayatarwa kan kur’ani, wanda za a gudanar a wannan birnin mai alfarma.
Babbar manufar samar wannan hanya ta harhada bayanai kan ayyukan kur’ani mai tsarki a karshen wannan zaman taro dai ita ce, kara karfafa gwiwar masu gudanar da bincike a bangarori daban-daban, har zuwa matakin digirin digirgir, wanda hakan ko shakka babu na daga cikin abubuwan da za su amfanar da al’umma a yanzu da kuma zamuna masu zuwa.
852258


captcha