Bangaren fikira, shugaban bangaren nazari kan sanin Allah a jami'ar Imam Sadiq (AS) ya bayyana idil fitr da cewa wani sakamako ne na dukaknin ayyukan bada da musulmi suka yi a cikin watan Ramadan mai alfarma.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, shugaban bangaren nazari kan sanin Allah a jami'ar Imam Sadiq amincin Allah ya tabbata a gare shi, ya bayyana idil fitr da cewa wani sakamako ne na dukaknin ayyukan bada da musulmi suka yi a cikin watan Ramadan mai alfarma da kuma kusanci da Allah day a samu.
Kamar yadda muka fada a cikin bayanin ayar da ta gabata, manzon Allah (SAW) ya umurci dukkanin musulmi da suka halarci yakin Uhud da su kara daura damara domin tunkarar rundunar mushrikai da suke nufin afkawa birnin madina, hakan ya sanya hatta wadanda suka ji raunuka ba a bar su a baya ba wajen aiwatar da wannan umurni na manzo.
Hakan ya jefa tsoro mai tsanani a cikin zukatan kafirai, inda suka ja baya, bayan sun kudiri aniyar yin kisan gilla a kan muslmi a cikin birnin Madina. Sai wannan ayar ta safka, domin yaba wa musulmi da kuma jaruntar da suka nuna.
851611