Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jagoran juyin juya halin muslunci na kasar Iran Ayatollah sayyid Khamenei cewa, jagoran ya taya al'ummar Iran da sauran al'ummar Iran masu girma murnar idin karamar salla sannan kuma ya kirayi mutane da su yi kokari wajen kiyaye abubuwan da suka samu cikin watan Ramalana mai alfarma yana mai cewa hakan zai tabbatar da ci gaban irin albarkokin da dacewa ta Ubangiji da aka samu a cikin watan tsawon shekara. Jagoran ya ci gaba da cewa: Kiyaye irin manyan nasarorin da aka samu a cikin watan Ramalana, irin su tsoron Allah, debe kewa da Alkur'ani, munajati da Ubangiji da kuma tsarkin zuciya, hakan lamari ne da zai kiyaye rayuwa ta daidaiku da zamantakewa da tabbatar da ita cikin aminci da tsaro sannan kuma a samu gudanar da so da kauna a cikin al'umma.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana gagarumar kasantuwar matasa, maza da mata da sauran kungiyoyi daban-daban na al'umma a lokacin ibadojin daren Lailatul kadari da sauran tarurruka na ibada na cikin watan Ramalanan a matsayin alamun da suke tabbatar tausayawa da kuma rahama ta Ubangiji sannan abubuwan da suke nuni da asalin yanayin al'ummar Iran. Jagoran ya ci gaba da cewa: Ta hanyar kwatanta tsoron Allah cikin ilimi da masaniya ta Ubangiji, matasa da sauran al'ummar kasar nan (Iran) suna ci gaba da tafiya a mikakken tafarki na Ubangiji, wanda hakan wata lada ce mai girma ga makomar wannan kasar da kuma al'ummar musulmi.
Har ila yau kuma a lokacin da yake gabatar da huduba ta biyu ta sallar idin, Ayatullah Khamenei ya gode da kuma jinjinawa al'ummar Iran sakamakon fitowar da suka yi kwansu da kwarkwatansu a lokacin zanga-zangar ranar Kudus yana mai cewa: Basira da himmar al'umma, wata ni'ima ce mai girma ta Ubangiji, wanda wajibi ne a jinjina mata.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan irin gagarumar fitowar da sauran al'ummar musulmi suke yi a ranar Kudus din a kasashe daban-daban na duniya, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce: Abubuwan da suke faruwa a yankin nan su ne suka sanya wasu daga cikin al'ummar musulmi kara fitowa wajen halartar zanga-zangar ranar Kudus da kuma shigowa cikin tawagar fada da ma'abota girman kai.
A wani bangare na hudubar sallar idin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi karin haske kan irin abubuwan da kasar Iran take bukata a halin yanzu, inda ya bayyana hadin kai da aiki kafada da kafada tsakanin bangarori daban-daban na al'umma, tsakanin mutane da jami'an gwamnati sannan da kuma tsakanin jami'an a tsakaninsa a matsayin bukata mai girma kuma ta asasi.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Sakamakon abubuwan da suke faruwa a wannan yankin, wani sabon shafi mai muhimmanci ne cikin tarihin duniya aka bude don haka wajibi ne al'umma da kuma jami'an gwamnati su yi taka tsantsan sannan kada su bari sabani da rarrabuwan kai ya zamanto abin da zai kawo musu cikas wajen sauke gagarumin da ke wuyansu.
852895