IQNA

Gaddafi Na Shirin Arcewa Zuwa Daya Daga Cikin Kasashen Makwaftan Libya

17:01 - September 03, 2011
Lambar Labari: 2180611
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Libya da ake kokarin hambararwa Mu'ammar Gaddafi na shirin arcewa zuwa day adaga cikin kasashen yammacin nahiyar Afirka da ke makwaftaka da kasar.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada gidan talabijin al'alam da daya daga cikin 'yan tawayen Libya ya bayyana cewa, a halin yanzu shugaban kasar da ake kokarin hambararwa Mu'ammar Gaddafi na shirin arcewa zuwa day adaga cikin kasashen yammacin nahiyar Afirka da ke makwaftaka da kasar inda ya ce zai fice ne daga yankin sabha.

A bangare guda kuma kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da zama na musamman domin tattauna batun halin da ake ciki a kasar Libiya.
Jakadan kasar Labanon a Majalisar Dinkin Duniya da a halin yanzu kasarsa ce ke jagorantar kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya Nuwaf Salam ya sanar da cewar a ranar 26 ga wannan wata na Satumba kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da zama na musamman domin tattauna batun matsaloli da irin halin da ake ciki a kasar Libiya.
Salam ya kara da cewa kafin zuwan ranar gudanar da zama na musamman kan kasar ta Libiya akwai yiyuwar kwamitin tsaron ya gudanar da wani zama dangane da kasar ta Libiya. A halin yanzu haka dai masu bore a Libiya suke iko da fiye da kashi 95 na kasar bayan da suka fatattaki shugaba Mu'ammar Gaddafi daga fadarsa da ke birnin Tripoli, kuma ya buya ba a san inda ya fake ba.

853397

captcha