Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sasrawa na yanar gizo na alwefaq an bayyana cewa, bababn malamin addinin uslunci na kasar Bahrain Ayatollah sheikh Isa Kasim ya bayyana cewa, kasha wani matashi dan shekaru goma sha hud da haihuwa da mahukuntan kasar Bahrain suka yi ya isa ya zama babban dalili na tabbatar da ta'addancin masarautan kasar ta Bahrain da 'yan mulkin mallaka suka kafa.
Dubban dubatan mutane ne suka fito zanga zanga a yankunan daban daban na kasar Bahrai don yin Allah wadai da kisan wani matshi dan shekara 14 wanda jami'an tsaron kasar Saudia suka yi a ranar laraba da ta gabata, jami'an tsaron kasar Saudiyya dai, sun kashe Ali Jawad ne a lokacinda suka jefa masa bututun hayaki mai sa hawaye a fuskarsa dab kusa da shi a garin Sitra.
Masu rajin kare hakkin bil'adama, jan'iyyun siyasa da yan adawa daga bangarori daban daban ne suka shiga zanga zangar, da kuma jana'izar matashin a jiya Alhamis.
A ranar laraba da ta gabat ce Sarki Hamid Bin Isa Al-khalifa ya yi alkawarin sake dukkan mutanen da gwamnatinsa ta take tsare da su tun lokacinda aka fara rikicin siyarsa kasar a farkon wannan shekara.
Kamar yadda ya yi alkawarin maida yan makaranta da aka kora, ko ma'aikatan da suka rasa ayyukansu duk sanadiyyar shiga cikin zangzangar nuna adawa da gwamnatinsa.
853416