Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alshawa an bayyana cewa, miliyoyin mutane da suka fito a ranar juma'ar karashen watan Ramadan mai alfarma hakan ya kara karfafa gwiwar mutanen da suke bore domin tabbatar da juyi a kasar tare da kawo karshen mulkin kama karya na shugaban kasar Ali Abdulalh Saleh da yake samun goyin bayan kasashen yammacin turai da 'yan korensu daga cikin shgabanni da sarakunan larabawa.
Rahotanni da suka fito daga wasu yankunan nakasar ta Yemen da ke fama da rikici sun bayyana cewa, akalla mutane 30 ne aka kashe a dauki ba dadin da ake yi tsakanin sojojin Yemen da 'yan kungiyar Al-Qa'ida na kasar a lardin Abyan da ke kudancin kasar ta Yemen.
Majiyar sojin kasar Yemen ta sanar da cewar gumurzu tsakanin sojojin Yemen da 'yan kungiyar Al-Qa'ida na kasar a lardin Abyan da kuma hare haren da jirgin saman yakin kasar Amurka da babu matuki ciki ya kaddamar kan sansanonin 'yan kungiyar ta Al-Qa'ida sun yi sanadiyyar halakar mayakan kungiyar Al-Qa'ida 30 a cikin kwanaki biyu wato ranakun laraba da alhamis da suka gabata. A gefe guda kuma manazarta sun bayyana cewar mafi yawan mutanen da hare haren jirgin saman Amurka ya kashe fararen hula ne.
A baya dai mahukuntan kasar Yemen sun musanta cewar Amurka tana yaki kai tsaye da 'yan kungiyar Al-Qa'ida a cikin kasar Yemen, amma rahoton baya bayan nan da kasar Amurka ta fitar ya tabbatar da cewa; tun a watan Yunin shekara ta 2010 sojojin Amurka suka fara yaki na kai tsaye da mayakan Al-Qaida a cikin kasar ta Yemen.
853182