IQNA

Masu Bore A Bahrain Za Koma Dandalin Lu'a-Lua Domin Ci Gaba Da Bore

17:54 - September 03, 2011
Lambar Labari: 2180632
Bangaren kasa da kasa, masu bore a kasar Bahrain sun sha alwashin komawa dandalin shahidai domin ci gaba da boren da suka fara na neman sauyi a cikin harkokin siyasa da mulkin kasar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a labarin da ya nakalto daga shfain sadarwa na yanar gizo na tashar al'alam an bayyana cewa, masu bore a kasar Bahrain sun sha alwashin komawa dandalin shahidai domin ci gaba da boren da suka fara na neman sauyi a cikin harkokin siyasa da mulkin kasar domin kawo karshen mulkin firnanci da kama karya na sarki Hamad Isa Ali-Khalifa.
Bayanin ya ci gaba da cewa daruruwan matasa masu bore na kasar Bahrain sun sha alwashin ci gaba da gudanar da zanga-zangarsu ta lumana kamar dai yadda suka fara, da nufin kawo karshen mulkin kama karya na 'yan mulkin mallaka da sarakunan kasar ke aiwatarwa.
Yanzu abin da matasan suke da niyar aiwatarwa shi ne komawa zuwa babban dandalin nan na tsakiyar birnin Manama, wanda aka fi sani da dandalin lu'a lua, wanda masu bore suka saka masa suna dandalin shahidai.
masu zanga-zangar bore a kasar Bahrain sun sha alwashin komawa dandalin shahidai domin ci gaba da boren da suka fara na neman sauyi a cikin harkokin siyasa da mulkin kasar maimakon zama karkashin azzalumai.
853167




captcha