Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alquds Al-arabi cewa, jaridar New York Times da ake bugawa a kasar Amurka ta bayyana a cikin wani rahotonta cewa an samu wasu bayanai da suka danganta shugaban kama karya na kasar Libya da hukumar liken asirin kasar Amurka a cikin mulkinsa kafin kasashen yammacin turai su hambara da shi.
Sabuwar gwamnatin rikon kwaryar Libya ta bada wa'adin zuwa gobe lahadi da safe ga mutanen garin Bani- Walid da su mika kai ko kuma fuskanci yaki.
Jami'in sojan da ke karkashin gwamnatin rikon kwaryar a garin Tarhuna, Abdur-Razaq Nadhuly ya fada a yau asabar cewa: "Masu bore sun gargadi shugabannin kabila na Bani Walid da su daga farar tuta ko kuma su fuskanci yaki daga nan zuwa sa'oi 24."
Daya daga cikin 'ya'yan hambararren shugaban kasar Libya Mu'ammar Khaddafi, Sa'idy yana da mafaka acikin garin na Bani Walid."
A gefe daya gwamnatin rikon kwaryar ta baiwa mutanen garin Sabha da sarta wa'adin mako guda da su mika wuya ko su ma su fuskanci yaki.
853717