IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani Mai tsarki A Kasar Saudiyya

18:54 - September 04, 2011
Lambar Labari: 2181210
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasar Saudiyya a mataki na kasa da kasa, wadda irinta ce ta biyu da ake gudanarwa bayar gasar da aka saba gudanarwa a kasar.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto rahoton da ke cewa shirin fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasar Saudiyya a mataki na kasa da kasa, wadda irinta ce ta biyu da ake gudanarwa bayar gasar da aka saba gudanarwa a kasar wadda ta saba daukar irin wannan taro.

Shin za a iya yarda da cewa Allah Madaukakin Sarki wanda ya halicce mu bisa asasi na ilimi da rahama da so da kauna, zai iya barin mu haka nan kawai ba tare da ya shiryar da mu hanyar sa’ada da samun farin ciki da kwanciyar hankali ba.

Alkur’ani mai girma dai a matsayinsa na Littafi na karshe da Allah Madaukakin Sarki Ya saukar da shi a matsayin littafi mai shiryar da bil’adama, sannan kuma ya nuna masa hanyar samun sa’ada da jin dadi kamar yadda kuma ya nuna masa abubuwan da za su iya halaka shi da haifar masa da matsaloli.

Na’am Alkur’ani mai girma ya yi bayanin ingantacciyar alaka ta iyali da zamantakewa, lamurra na shari’a da kyawawan halaye, bukatu na jiki da ruhi, nauyi na daidaiku da jama’a, ingantattu da kuma sunoni na kuskure da suke cikin al’umma, dokoki na kudi da tattalin arziki da sauran lamurra masu yawa na daban.

Duk da cewa a cikin Alkur'ani mai girma, an kawo labarai da kissoshin yakukuwa da rikice-rikice da kuma yadda yaruwar wadansu maza da mata na al'ummomin da suka gabata ta kasance, to amma Alkur'ani dai ba littafi ne na labari da kissoshi ba, face dai littafi ne na daukan darussa saboda rayuwar al'ummomin wannan zamanin.

A saboda haka ne ma aka sanya wa wannan littafin suna 'Alkur'ani' wato littafin abin karantawa, wato littafin da wajibi ne a karanta shi sai dai ba wai kawai karatu da harshe ba irin yadda ake karantar da yara a makaranta, face dai karatu tare da tunani cikin abubuwan da ake karantawa, duk da cewa an bukace mu din da mu karanta shi din kamar yadda ake karantawar.

853633
captcha