IQNA

Za A Bude Cibiyoyin Nuna Kayan Abincin Halal A Yankin Bashqirestan

20:25 - September 04, 2011
Lambar Labari: 2181240
Bnagaren siyasa da zamantakewa, ana shirin bude cibiyoyin nuna kayan abincin halal a cikin addinin muslunci a Bashqirestan da nufin jawo hankulan mutanen da suke da bukatuwa zuwa ga sani ababen halal daidai da koyarwar wannan addini.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na slam.ru an bayyana cewa, za a bude cibiyoyin nuna kayan abincin halal a cikin addinin muslunci a Bashqirestan da nufin jawo hankulan mutanen da suke da bukatar sanin abincin halal wanda addinin muslunci ya halasta bisa koyarwarsa, kuma za arika sayar da abincin ne da kima mai saukin farashi.
Ya zuwa yanzu haka dai kimanin kamnoni 40 ne daga cikin kamfanonin kasar suka sanar cewa a shirye suke da su shiga cikin wannan shiri domin samar da abincin halal, wannda kuma tuni aka bayar da dam aga kamfanonin da suke da bukatar shiga shirin da su yi rijista da hukumar da ke kula da shiri.
Daga cikin muh8imman abubuwan da wannan shiri zai mayar da hanakali kansa na daga kayand da zai rika samarwa har da kayan abinci na alkama da kuma kayan sanyawa wato tufafi, bayan haka kuma akwai kayan tsaraba na ciye-ciye da kuma kayan zaki da dai sauransu.
853728

captcha