Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, shugaban cibiyar bunkasa harkokin al'adu yana fada yunkurin da musulmi suke yi a cikin kasashen larabawa na bukatar yin tsayuwa domin kare manufar yunkurin juyin, domin kauce wa fadawa cikin tarkon makiya addini da ake bayyana kansu tamkar masu goyon musulmi da suke son nuna cewa su masu goyon bayan abin da ke faruwa ne.
Mohammad Bagher Khoramshad ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halartar wani taro na karawa juna sani na Iraniyawa mazauna kasashen ketare, dangane da matsyin al'adu da ilimin muslunci a duniyarmu ta yau, wani rahoton kuma ya yi nuni da cewa, ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana jin dadinta kan matakin da kasar ta dauka na koran jakadan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila daga birnin ankara fadar mulkin kasar,
A bayanin da ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar ta bayyana tsananin rashin jin dadinta kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi tasiri wajen canja akalar rahoton kwamitin da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa domin gudanar da bincike dangane da harin wuce gona da iri da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan jirgin ruwan kasar.
Har ila yau bayanin na ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki matakin hana tsoma bakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a duk wani aikin da take gudanarwa musamman a bangaren rahoto ko bincike da wani kwamiti na Majalisar zai gudanar.
A watan Mayun shekara tda ta gabata ne sojojin gwamnatin yahudawa suka kai harin wuce gona da iri kan jirgin ruwan kasar turkiyya da ke dauke da kayayyakin jin kai ga al'ummar Palasdinawa da ke Zirin Gaza, inda suka kashe Turkawa 9, kuma kwamitin majalisar dinkin duniya da ke bincike kan lamarin ya goya baya ga H.K.Isra'ila saboda tasirin da ta yi a ayyukan Majalisar Dinkin Duniya.
854343