IQNA

Babban Malamin Jami'ar Azhar Ya Mayar Da Martani Kan Neman Sakin Mubarak

16:50 - September 05, 2011
Lambar Labari: 2181880
Bangaren kasa da kasa, babban malamin jami'ar Azhar a kasar masar ya mayar da martini kan wani malamin yahudawa da ya yi kira da a yi wa tsohon shygaban mulkin kama karya na kasar Masar Husni Mubarak afwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani bayani daga shafin sadarwa na yanar gizo na NASIJ cewa, a cikin wani bayani da ya fitar babban malamin jami'ar Azhar a kasar masar ya mayar da martini kan wani malamin yahudawa da ya yi kira da a yi wa tsohon shygaban mulkin kama karya na kasar Masar Husni Mubarak afwa kan ayyukan day a tafka.
Ministan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ya sanar da cewa; haramtacciyar kasar Isra'ila ba zata amince kasar Masar ta jibge sojoji masu yawa a tsibirin Sina mallakin kasar ta Masar ba.
Jaridar shafinta na Internet ta bayyana cewar a jiya asabar ministan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila Ihud Barak ya sanar da cewar haramtacciyar kasar Isra'ila ba zata amince da shirin kasar Masar na jibge sojoji masu tarin yawa a tsibirin Sina da ke kusa da kan iyaka da Isra'ila ba.
A gefe guda kuma da ake bugawa a kasar Birtaniya a fitowarta ta ranar Juma'a ta bayyana cewa; Ihud Barak ya furta cewar idan gwamnatin Masar zata jibge sojojin masu yawa a tsibirin na Sina da nufin magance tashe tashen hankula da suke faruwa a kan iyakarta da haramtacciyar kasar Isra'ila ce, to babu matsala zata iya jibge sojojin domin hakan zai zame amfani ne ga Isra'ila.
854280

captcha