Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo da ke cewa, daya daga cikin malaman addini a Saudiyya Sheikh Hassan Saffar ya ce bayar da fatawar kafirta musulmi da kuma halasta jininsu da wani bangaren musulmi ke yi hakan tamkar aikata laifin isan ne wanda ake kan mutanen da ba su ji ba su gani ba domin banbancin akida ko fahimta a cikin addinin musulunci.
Malamin ya ci gaba da cewa babban abin ban takaici ne yadda wasu daga cikin musulmi suke yin amfani da damar da suke da ita wajen tunzura wani bangare a kan wani, domin kawai suna ganin cewa su kadai ne musulmi wancan daya bangaren ba musulmi ne, ya ce koda haka ne to menen na halasta jinin musulmi.
Wanann matasala da musulmi suke fama da ita ta samo asali daga munanan akidu na maboya tafarkin wahabiyanci, ta zama ita ce bababn abin da ke ci musu tuwo a kwarya, domin kuwa ana kallonsu a matsayin masu wakiltar addini a duniyarmu ta yau.
Wani malami ya ce bayar da fatawar kafirta musulmi da kuma halasta jininsu da wani bangaren musulmi ke yi hakan tamkar aikata laifin isan ne wanda ake kan mutanen da ba su ji ba su gani ba domin banbancin akida da ake da ita, wanda kuma hakan ba dalili neb a.
854183