Bangaren kasa da kasa, babban malamin addinin muslunci na kasar Iraki Aytaollah Sistani ya zanta da babban malamin addinin na Bahrain Aytaollah Isa Kasem dangane da abubuwan da suke faruwa kan mabiya tafarkin iayalan gidan manzo a kasar.
Kamfanin diallcnin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labar da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na albayan an bayyana cewa, malamin addinin muslunci na kasar Iraki Aytaollah Sistani ya zanta da babban malamin addinin na Bahrain Aytaollah Isa Kasem dangane da abubuwan da suke faruwa kan mabiya tafarkin iyalan gidan manzo a kasar ta Bahrain na muzgunawa da cutarwa daga masarautar Ali-khalifa.
Aytaollah Sistani ya bukaci Karin haske dangane da abin da ake ciki na murkushe masu bore da karfin tuwo da mahukunta Bahrain suke dauka, domin sanin irin matakin da za aiya dauka na kawo karshen wannan mummunan aiki na gidana sarautar da turawan mulkin mallaka suka kafa.
Tun kafin wannan lokacin dai Ayatollah Isa Kasim ya bayyana wannan mataki da cewa ya yi hannun riga duk wani addini, kuma wajibi mahukuntan kasar Bahrain su dauki matakan da suka dace domin yin gyara a cikin harkokin mulkin kasar ta fuskar siyasa.
854195