Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa JafariNews an bayyana cewa, Sayyid Muktada Sadr jagora magoya bayan sadr a kasar Iraki ya ja kunnen jami'an tsaron kasar Bahrain da su shiga taitayinsu kan kisan kiyashin da suke kan musulmin kasar da suke neman sauyi a cikin harkokin siyasa da mulkin kasar, wadda mutanenta akasarinsu magoya bayan mazhabar shi'a ne.
Wani rahoton kuma na daban yana cewa, Palasdinawa a yankin Gaza na kasar Palasdinu sun gudanar da zanga zangar yin Allah wadai da rahoton majalisar dinkin duniya wanda ya nuna rashin adalci kan harin da hramtacciyar kasar Isra'ila ta kaiwa tawagar jiragen ruwa dauke da kayakin agajia zuwa yankin.
Komitin bincike da kuma gano gaskiya wandda majalisar dinkin duniya ta kafa karkashin Jagorancin Jafrin Bolmar don gano yadda sojojin hramtacciyar kasar Isra'ila suka kaiwa ayarin jiragen ruwa dauke da kayakin agaji zuwa yankin gaza a ranar 31 ga watan mayun shekara ta ya bayyana cewa hramtacciyar kasar Isra'ila bata da laifi a wannan harin.
Palasdinawan wadanda suka taru a tsakiyar yankin na Gaza sun bayyana cewa kubutar hramtacciyar kasar Isra'ila daga laifi a wannan harin ya nuna cewa majalisar dinkin duniya ta halatta kofar ragon da takewa yankin kimani shekaru 4 da suka gabata.
ar'ila yau Palasdinawan sun yaba da matakan da kasar turkiyya ta dauka na korar jakadar daga Ankara da kuma rage mu'amala a tsakanin kasashen biyu.
854089