IQNA

Banbanci Tsakanin Goyon Bayan Da Masu Bore Suke Samu A Kasashen Larabawa

17:09 - September 06, 2011
Lambar Labari: 2182574
Bangaren kasa da kasa, masu bore a cikin kasashen larabawa a cikin lokutan nan suna ganin banbamci dangane da yadda kasashen yammacinda kuma na larabawa 'yan amshin shatan turai suke bayarwa da kuma na kasashen musulmi.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an sheda cewa, cikin kasashen larabawa a cikin lokutan nan suna ganin banbamci dangane da yadda kasashen yammacinda kuma na larabawa 'yan amshin shatan turai suke bayarwa da kuma na kasashen musulmi da suke yankin da wajensa a cikin wadannan lokuta.

Wani labarin kuma yana cewa, yau talata ne Majalisar Kwararru mai zabe tare da sanya ido kan ayyukan Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ta buda zamanta karo na goma a cikin zauren tsohuwar Majalisar Dokokin kasar ta Iran da ke nan birnin Tehran domin tattauna muhimman batutu da ke gabanta.

Wannan Majalisar dai tana da wakilai masana wadannan aka zabo a kan wa'adin aiki na shekaru hudu kowannen su, kuma su ne ke da alhakin sanya ido kan yadda Jagora ke tafiyar da ayyukansa da kuma tabbatar da cewa sun dace da manufofi na tsarin juyin juya halin musulunci wanda kasar ta dogara a kai.

Majalisar wacce a halin yanzu take a karkashin jagorancin Ayyatullah Mahdavi Kani, dole ne a karkashin dokokin da ke tafiyar da ita ta gudanar da zama sau biyu a shekara, kuma dole zaman ya share akalla tsawon kwanaki biyu.

Daga cikin wadanda za su gabatar da jawabi a wurin buda zaman Majalisar sun hada har da Shugabanta da kuma ministan tara bayanan asiri na kasar ta Iran wanda shi ma daya ne daga cikin wadanda suka taka gagarumar raya ta wannan fuska.

854875


captcha