Kamfanin dilalcnin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISEECO inda aka bayyana cewa an buga tare da yada wani littafin na hukumar bunkasa harkokin ilimi ta duniya da yin gyara kan istilahohi na kur'ani mai tsarki ta yadda zai amfani musulmi a duk inda suke cikin duniyar nan.
A koda yaushe a cikin al'ummomi, mutanen da suke su ne a matsayi tsaka tsaki, suna yin biyayya ne ga manya daga cikin al'umma, wannan ne ya sanya idan manya suka gyaru sai al'umma ta gyaru, idan kuma suka lalace hakan zai yi tasiri wajen lalacewar al'ummar.
Daya daga cikin abubuwan da Allah ya dora ma masana ma'abuta ilimi daga cikin al'umma shi ne, su bayyana ma mutane abin da yake daidai da wanda ba daidai ba, su gayama mutane abin da yake gaskiya, kada su boye ayoyin Allah, domin boye gaskiya da kange mutane daga fahimtar abin da ya zo a cikin umurnin babban laifi ne.
Kamar yadda ya tabbata a cikin tarihi cewa, masana daga cikin wadanda aka baiwa littafi sun yi shir da bakunansu dangane da busharar da ta zo a cikin littafan attauara da linjila, kan bayyanar manzon karshe yadda suka bar mutanensu cikin duhun jahilci, maimakon haka ma a hankali-a hakali sun yi ta cire duk wata bushara kan bayyanar manzon Allah na karshe a cikin littafan na su, domin kada su rasa mabiya.
854466