Bangaren kasa da kasa, farkawar da musulmi suka yi a halin yanzu domin kalubalantar azzaluman shugabanninsu musamman acikin kasashen larabawa da suke karkashin mulkin fir'ananci na sarakunansu, shi ne bababn lamari a yankin gabas ta tsakiya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Hojjatul islam Akhtari babban daraktan majma'ar Ahlul bait (AS) ya sheda cewa, farkawar da musulmi suka yi a halin yanzu domin kalubalantar azzaluman shugabanninsu musamman acikin kasashen larabawa da suke karkashin mulkin fir'ananci na sarakunansu, shi ne bababn lamari a yankin gabas ta tsakiya baki daya.
Wani rahoton kuma ya yi nuni da cewa jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da kame wasu 'yan kungiyar a biyar dauke da bama bamai da makamai a cikin kasar Iran babban kwamandan dakarun tsaron kasa a lardin kirmon da ke kudu maso gabashin kasar Iran Brigadier Janar Husain Janariyon a jiya talata ya sanar da cafke wasu 'yan kungiyar biyar dauke da tarin makamai da bama bamai gami da na'urori da bayanan sirri a lardin kirmon, kuma bincike da tabbatar da cewa uku daga cikin mutanen Iraniyawa ne sauran biyu kuma baki ne 'yan kasar waje, kuma suna shirin aiwatar da hare haren ta'addanci ne a cikin kasar Iran.
Har ila yau Janar Janariyon ya kara da cewa; bayan gudanar da bincike kan mutanen an kai ga gano wasu tarin makamai da bama bamai da kuma na'urori da aka shigo da su cikin kasar Iran, inda aka boye a lardin wanda yake yamma maso kudancin kasar Iran, yanzu haka dai ana ci gaba da sanya ido a cikin wadannan yankuna.
856417