Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa a wani labarin da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo an sheda cewa, Hojjatil Islam Muhammad hassa Akhtari ya bayyana cewa babbar cibiyar nan ta Ahlul-bait (AS) ta gudanar da wani zama na manema labarai domin bayyana ayyukan da take gudanarwa a karo na biyar wanda ke samun halartar masana da manema labarai daga kasashen duniya wanda kuma daman ana gudanarwa.
Wasu daga cikin mabiyan annabi Musa da annabi Isa da su ke son tabbatar da cewa addininsu ne kadai gaskiya da kuma rusa sauran addinai. Abinda su ke riyawa kenan har ta kai suna cewa annabi Ibrahim da kuma sauran annabawan da su ka zo bayansa suna kan addininsu ne.
Ga shi kuwa ta fuskar tarihi annabi Musa da annabi Isa sun zu ne bayan wadancan annabawan, saboda haka abinda wadannan mutanen su ke riyawa ba komai ba ne sai bakin kishi mara dalili da kuma nuna wariya, idan ba wannan ba ba su da wani dalilin da za su iya dogaro da shi.
Al'kur'ani yana bayyana gurbata gaskiya ko boye ta a matsayin zalunci mai girma, musamman ma dai idan ya kai ga karkacewar akida da kuma tunanin zuriyar da ta biyo baya da kuma zamunna mabanbanta, ya kuma hana al'adun bil'adama su bunkasa su kai ga kamala. 855562