IQNA

Jakadan Isra'ila A Cairo Ya Gudu Zuwa Birnin Tel Aviv

14:21 - September 10, 2011
Lambar Labari: 2184428
Bangaren kasa da kasa, jakadan Isra'ila a birnin alkahira na kasar Masar ya gudu zuwa birnin Tel Aviv bayan da dubban daruruwan matasan kasar Masar suka afka ofishin jakdancinsu da ke birnin a jiya Juma'a.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalt daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar al-alam cewa, yanzu haka dai jakadan Isra'ila a birnin alkahira na kasar Masar ya gudu zuwa birnin Tel Aviv bayan da dubban daruruwan matasan kasar Masar suka afka ofishin jakdancinsu da ke birnin a jiya Juma'a a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar neman a kori jakadan haramtacciyar kasar da ke zaune a birnin Cairo.

Rahotanni daga birnin na Alkahira sun yi nuni da cewa matasan sun yi kira da a gudanar da wannan jerin gwano ne daga babban dandalin nan da ke tsakiyar birnin, bayan da suka kammala sallar Juma'a sun nufi ofishin jakadancin Isara'ila, inda suka kada bangon da aka gina domin bayar da kariya ga yahudawa.

Haka nan kuma dubban daruruwan martasan sun taru a bababn filin wasannin na birnin cairo, inda aka gabatar da laccoci da suke kiran majalisar sojin kasar tad a gaggauta daukar matakan kawo sauyi na komawa zuwa tsarin demokradiyya.

Labarin baya0bayan nan jakadan Isra'ila a birnin alkahira na kasar Masar ya gudu zuwa birnin Tel Aviv bayan da dubban daruruwan matasan kasar Masar suka afka ofishin jakdancin, kuma hakan ya tayar da hankalin Amurka matuka.

857532


.

captcha