Bangaren kasa da kasa, 'yan tawayen kasar Libya da suke dauke da makamai sun shiga garin Bani Walid wanda shi ne gari na biyun karshe da ke hannun magoya bayan Mu'ammar gaddafi shuban mulkin kama karya na kasar Libya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na al-intiqad an bayyana cewa, 'yan tawayen kasar Libya da suke dauke da makamai sun shiga garin Bani Walid wanda shi ne gari na biyun karshe da ke hannun magoya bayan Mu'ammar gaddafi shuban mulkin kama karya na kasar wanda a halin yanzu ake nemansa ruwa ajallo, amma ba a ganshi ba ko jin duriyarsa.
A wani labarin kuma a karon farko tun bayan faduwar gwamnatin Gaddafi a kasar Libiya shugaban Majalisar Wucin Gadi da ke wakiltan masu bore a kasar Mustafa Abdul-Jalil ya shiga birnin Tripoli fadar mulkin kasar ta Libiya a jiya asabar.
Ministan harkokin cikin gidan kasar Libiya a Majalisar Wucin Gadin kasar Ahmad Dharad ya bayyana cewar zuwan Mustafa Abdul-Jalil cikin birnin Tripoli dalili ne da ke tabbatar da cewar mulkin kama karya na Mu'ammar Gaddafi ya kawo karshe a kasar Libiya.
Daruruwan jama'a ne suka tarbi shugaban Majalisar Wucin Gadin Mustafa Abdul-Jalil bayan isarsa birnin na Tripoli karkashin tsauraran matakan tsaro.
857755