Kamfanin dilalcnin labaran iqna ya habarta cewa bangaren yad alabaransa ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar al-wefaq cewa, na'ibin limami kuma wanda ya jagoranci sallar juma'a abirnin Tehran ya bayyana cewa zalunci da danniyar shugabanni da sarakunan kasashen larabawa ce ta jawo boren da al'ummomi suke yi domin kawo karshen wannan zalunci da danniya da kuma babakere kana bin da shugabanninsu ke yi.
Acikin shirin baya mun ambata cewa, musulunci yana yin wasici da akiyaye hakkokin mu’alama ta cinikayya wacce babu kudi lakadan aciki haka nan kuma a cikin bada bashi, ta yadda za a rubuta su, kuma a kafa shedu guda biyu, saboda ya zamana an warware matsala idan aka sami kuskure ko mantuwa ko kuwa daya bangaren ya yi inkari.
Yadda musulunci ya bada muhimmanci akan wannan lamarin ta kai ga yana yin wasici da a rubuta bashi koda ana kan tafiya ne. Idan kuma ba a sami wanda zai rubuta ba to a karbi jingina, sai dai wajibi ne ga wanda ya karbi jingina da wanda ya bayar su san da cewa abinda ya ke hannuwansu amana ce, kuma wajibi ne su maida wannan amanar a lokacin da ya dace ga mai ita.
Jinginar da ta ke hannun wanda ya bada bashi amana ce kuma bashi da hakkin cin moriyarta ta hanyar da bata dace ba. Kuma wajibi ne a gare shi ya yi kokarin kiyayeta ta yadda idan wanda ya karbi bashi ya biyashi bashinsa ya maida masa abinda ya karba jingina sumul kalau kamar yadda ya ke. 857683