Kamfanin dilalcnin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na intiqad cewa, an daga tutuna da ke nuna goyon bayan musulmi ga al'umamr palastinu dangane da zaluncin da suke fuskanta daga sarakuna da suhabanninsu a cikin lokutannan da muke ciki musamman a kasashen larabawa.
A mahanga ta musulunci, duniya ta yi kama da makaranta wacce a tsawon tarihi Ubangiji ya ke aiko da malamai da su ne manzanni domin su shiryar da mutane da kuma yi musu tarbiyya.
Kowane daga cikin wadannan annabawan sun koyar da mutane a cikin wani aji na tarihi sun kuma daukaka matsayinsu daidai gwargwado har zuwa lokacin da hankalin mutum ya kai munzalin da zai iya karbar cikakken tsari daga Ubangiji, sai Ubangiji ya aiko da cikamakin annabawa, manzon Allah Muhammad (s.a.w.a)
A saboda haka duk wani musulmi ya yi imani da dukkanin annabawan Allah da kuma dukkanin littatafan da ya saukar kuma baya banbanta tsakanin manzannin Allah.
857584