Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na peterleemail cewa, an nuna wasu kwafin kur'ani mai tsarki da aka tarjama a cikin harshen turancin Ingilishi a kasar Birtaniya da nufin kara bunkasa fahimtar masu Magana da wannan harshen kan muslunci da kuma koyarwarsa kan dukkanin bangarori da kur'ani mai tsarki ya yi ishara da su.
Jinginar da ta ke hannun wanda ya bada bashi amana ce kuma bashi da hakkin cin moriyarta ta hanyar da bata dace ba. Kuma wajibi ne a gare shi ya yi kokarin kiyayeta ta yadda idan wanda ya karbi bashi ya biyashi bashinsa ya maida masa abinda ya karba jingina sumul kalau kamar yadda ya ke.
Shi ma wanda ya ci bashi abin amincewa ne a wurin wanda ya ba shi bashi, saboda haka wajibi ne ya cika alkawalii ya maida amanar da aka bashi, kada ya cutar da wanda ya bashi bashin, musamman mai ace wanda ya bashi bashin nan ya amince masa matuka, idan kuma babu wannan to ya ji tsoron Allah kada ya take masa hakki.
A karshen ayar an yi kira ga dukkanin muminai da kada su yi sassauci da hakkokin mutane, domin kuwa Allah yana da masaniya akan abinda ya ke yawo acikin zukata. Take hakkin wani kuwa zunubi ne mai girman gaske. Domin kuwa yana gurbata ruhin mutum. 857678