IQNA

Kafa Kwamitin Bincike Kan Sanin Makomar Imam Musa Sadr

21:23 - September 11, 2011
Lambar Labari: 2185278
Bangaren kasa da kasa, an kafa wani kwamitin binccike domin sanin makomar Imam Musa Sadr shugaban majalisar mabiya tarfarkin iyalan gidan manzon allah a kasar Lebanon wanda zai fara aikinsa a cikin ‘yan kwanakin nan.
Kamfanin dilalncin labaran iqna yahabarta cewa ya nakalto wani rahoto da ke cewa mataimakin shugaban majalisar mazhabar shia Aytaollah Amir Qabalan ya sheda cewa, an kafa wani kwamitin binccike domin sanin makomar Imam Musa Sadr shugaban majalisar mabiya tarfarkin iyalan gidan manzon allah a kasar Lebanon wanda zai fara aikinsa a cikin ‘yan kwanakin nan da nufin sanin inda Imam yake idan yana raye.
Abin takaici ne cewa wasu mabiya addinan da ba su da cikakkiyar masaniya akan koyarwar addini, suna zaton cewa suna da matsayi na musamman a wurin Ubangji, kuma da su kadai ne Ubangiji ya damu, kuma saboda su kadai ne ya aiko annabawa, saboda haka ba a shirye su ke ba su yi imani da wasu annabawa kuma ba su cikin masu yi musu biyayya.
Allah madaukakin sarki ba shi da dangantaka da wata kabila ko da wasu iyalai domin kuwa a wurin kowa da kowa daidai wa daida su ke. Abu guda daya wanda ya ke sa mutane su kusance shi ko su yi nisa da shi shi ne aikin da su ke yi, kuma kowane mutum aiki da ya yi ne yake bibiyyarsa.
Shakka babu aikin da ya ke zama karbabbe shi ne wanda aka yi da tsarkin niyya saboda Allah, domin kuwa wannan irin aikin yana nuni ne da imani na hakika da kuma nesantar duk wani nau'i na shirka.
858038
captcha