IQNA

Mai Tarjamar Kur’ani Dole Ne Ya Yi La’akari Da Banbamcin Yanayin Harsuna

21:24 - September 11, 2011
Lambar Labari: 2185284
Bangaren kasa da kasa, mai tarjamar kur’ani mai tsarki dole ne ya yi la’akari abubuwa da dama a lokacin tarjamarsa da hakan ya hada da yanayin banbancin harsuna da al’adun mutane masu magana da harshen da yake tarjama.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa mai tarjamar kur’ani mai tsarki dole ne ya yi la’akari abubuwa da dama a lokacin tarjamarsa da hakan ya hada da yanayin banbancin harsuna da al’adun mutane masu magana da harshen da yake tarjama domin kada a samu kuran fahimta ga mai karatu.
Na biyu shi ne cewa, mushrikan makka sun maida ka'aba ta zama wurin bautar gumaka, idan ma'aiki ya tsaya a masallacin harami yana fuskantar ka'aba to a hakikanin gaskiya yana fuskantar gumakan da su ke cikin ka'abar ne.
Bayan yin hijira zuwa madina an dauki wasu watanni musulmi suna fuskantar Baitul mkaddas suna yin salla har zuwa lokacin da yahudawa su ka maida batun ya zama na suka suna fadin cewa, mu ku ke yi wa biyayya, ba ku cin gashin kanku, domin kuwa ba ku da alkibla taku ta kanku.
Wannan cin zarafin ya fusata ma'aiki da kuma musulmi.
Umarni ya zo daga Ubangiji akan sauya alkibla, a yayin da manzon Allah ya ke cikin yin sallar azahar a cikin masallaci. Mala'ika Jibra'ilu ya zo da umarni ga annabi da ya juya alkibla zuwa ga Ka'aba. saboda haka ne ake kiran wannan masallacin da sunan "masallacin alkibloli biyu".
Sai dai yahuawa wadanda aikinsu shi ne yin suka, sun sake yin wata sukar su ka fadawa musulmi cewa, idan alkiblarku ta baya daidai ce to me ya sa ku ka sauya ta? Idan kuwa wannan sabuwar alkiblar ce daidai to ya me ya sa tun da farko ku ka rika fuskantar Baitul Mukaddas.
857555

captcha