Bangaren kasa da kasa, ci gaba da fadaka da musulmi suke yi yanzu musamman ma a cikin kasashen larabawa zai kara zaburar da dukaknin 'yantattau masu neman sauyi na adalci da kubuta daga danniyar azzalumai a kasashen duniya.
Kmafanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, tsohon pira ministan kasar Iraki Dr. Ibrahim jafari ya bayyana cewa ci gaba da fadaka da musulmi suke yi yanzu musamman ma a cikin kasashen larabawa zai kara zaburar da dukaknin 'yantattau masu neman sauyi na adalci da kubuta daga danniyar azzalumai a kasashen duniya kamar dai yadda muke gani.
Ya ci gaba da cewa dole ne al'ummomin duniya su kwana da sanin cewa rayuwa cikin 'yanci ita rayuwa ta mutunci, matukar dai ba a bari mutane suka samu 'yancin gudanar da rayuearsu da amfana daga arzikin da Allay a basu ba, to kuwa shugabannin irin wadannan kasashe za su ci gaba da ganin bore daga al'ummominsu, abin da ke faruwa yanzu a kasashen musulmi da na larabawa ya isa yazam aya.
Wannan ci gaba da fadaka da musulmi suke yi yanzu musamman ma a cikin kasashen larabawa zai kara zaburar da dukaknin 'yantattau masu neman sauyi na adalci da kubuta daga danniyar azzalumai a kasashen duniya musulmi ko ba musulmi, larabawa ne ko ba su ba.
859125