Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na aynar gizo na OCI cewa, wannan kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta fitar da wani bayani a daidai lokacin da ake tunawa da harin sha daya ga watan satumba da aka kai kasar Amurka a cikin sheara ta dubu biyu da daya wato 2001 da ta gabata.
Bayanin ya ci gaba da cewa a daidai lokacin hukumomi a kasar Amurka suke juyayin harin 11-satumban -2001, shugaban kasar Iran Dr. Najad ya ce kasar Amurka ta yi amfani da harin satumba -2001 ne kawai don ta mamaye kasashen Afganistan da Iraqi. Da kuma jawo ya zuwa yanzu rayukammu mutane fiye da miliyon daya.
Kamafanin dillancin labaran Mehr na nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya ce shugaban ya bayyana haka ne a bukin bude taron kungiyar "Majma Ahlul –bait al-alami- wanda aka fara a yau a nan Tehran, shugaban ya jadda matsayin kasarsa na kin amincewa da dukaknin matakan da kasashe masu girman kai suke dauka na takurawa musulmi da sunan yaki da ta'addanci.
Kasashen duniya da dama sun nuna taikaicinsu da yadda gweamnatin Amurka ta yi amfani da batun harin sha day aga watan satumba wajen kaddamar da yaki kan wasu kasashe domin kawai ta cimma burinta na mamaye arzikinsu da kashensu. 859064