IQNA

Hari Kan Ofishin Jakadancin Isra'ila A Cairo Zai Gaggauta 'Yantar Da palastinu

14:07 - September 12, 2011
Lambar Labari: 2185842
Bangaren kasa da kasa, harin da masu bore suka kai kan ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra'ila da ke birnin Alkahira wata lama ce ta gaggauta 'yanto yankin palastinu daga mammayar yahudawa.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin di Alalam cewa harin da masu bore suka kai kan ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra'ila da ke birnin Alkahira wata lama ce ta gaggauta 'yanto yankin palastinu daga mammayar yahudawa tun tsawon shrkaru da suka gabata.

Bayanin ya ci gab ada cewa fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ya bayyana cewar haramtacciyar kasar Isra'ila zata ci gaba da mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da ke tsakaninta da kasar Masar a furucin da ya fito daga bakin fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kwana daya bayan harin da jama'ar kasar Masar suka kai kan ofishin jakadancin h.k.Isra'ila da ke birnin Alkahira.

Benyamin Netanyahu ya bayyana cewar haramtacciyar kasar Isra'ila zata ci gaba da mutunta yaejejeniyar zaman lafiya da ke tsakaninta da kasar Masar domin hakan shi ne masalahar kasashen biyu, kuma gwamnatin h.k.Isra'ila tana ci gaba da tuntubar gwamnatin Masar domin ganin jakadan Isra'ila ya koma kasar ta Masar cikin hanzari.
Netanyahu ya kuma jinjinawa gwamnatin Masar kan matakin da ta dauka na 'yanto jami'an tsaron h.k.Isra'ila shida da aka yi garkuwa da su a cikin ofishin jakadancinta da ke kasar ta Masar, kamar yadda ya yaba wa shugaban kasar Amurka Barak Obama kan tsoma bakin da ya yi na ganin gwamnatin Masar ta hanzarta daukan matakin shawo kan masu zanga zangar da suka killace ofishin jakadancin h.kasar ta Isra'ila da ke Masar.
858198

captcha