Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a wani jawabi day a gabatar a gaban taron kasa da kasa kan addinai da al'adu mataimakin shugaban cibiyar yada al'adu da ilmomin muslunci ya bayyana cewa dole ne a samu fahimtar juna tsakanin dukkanin mabiya addinai na duniya kafin tabbatar sulhu da adalci a bayan kasa, matukar dai ana son al'ummomi su zauna lafiya.
Bayanin ya ci gaba da cewa ya zo a cikin littafai da dama na tafsirin kur'ani mai tsarki cewa, manzon Allah ya aike da wata wasika zuwa ga kabilar yahudawa da ke gefen birnin Madina, yana kiransu zuwa ga musulunci, da yin sallah da kuma bayar da zakka da ciyar da dukiyoyinsu domin Allah, sai shugaban kabilar yahuwan yake yin izgili da wannan wasika, har ma yana cewa: Allah shi ne mabukaci a wurinmu, mu ba mu ne mabukata ba, ya roke mu da mu ba shi kudi, ya yi mana alkawarin cewa a ranar kiyama zai mayar mana da yawa.
Bayan wannan furuci na shugaban yahudawan ne sai wannan aya mai albarka ta safka, inda Allah ya sheda ma manzonsa cewa wadanda suka yi wannan furuci za su shiga cikin azabar jahammana a ranar kiyama.
859677