Bangaren kasa da kasa, pira minister palastinu a yankin zirin gaza Isma'ila Haniyya ya taya dukkanin al'ummar kasar Libya murnar samun nasarar kawo karshen mulkin kama karya na Mu'ammar Gaddafi wanda ya kwashe tsawon shekaru an mulkin kama a kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Al-manar cewa Isma'ila Haniyya ya taya dukkanin al'ummar kasar Libya murnar samun nasarar kawo karshen mulkin kama karya na Mu'ammar Gaddafi wanda ya kwashe tsawon shekaru an mulkin kama a kasar tare da murkushe duk mai adaw ada shi da karfin tuwo.
Sakataren Kungiyar Tsaro ta Nato Anders Fogh Rasmussen ya ce sojojinsu za su ci gaba da kai hare-hare a cikin kasar Libya sai zuwa lokacin da al'ummar kasar ta kasance a cikin yanayi na tsaro, kalaman na Rasmussen dai sun zo ne a daidai lokacin da sojojin 'yan tawaye da suka yi yunkurin kama birnin Bani Walid da ke hannun magoya bayan kanar Kaddafi ke ci gaba da fuskantar turjiya, lamarin da ya tilasta wa 'yan tawayen ja da baya tare kuma da neman taimakon kungiyar ta Nato domin rage karfin baraden na Kanar Kaddafi da suka ja daga a birnin.
Da farko dai 'yan tawayen sun takaita karfin da sojojin na kanar Mu'ammar Kaddafi suke da shi a birnin na Bani Walid, inda suka yi kokarin kutsawa a cikinsa tun a shekaranjiya asabar. A daya bangare kuwa Firaminsitan kasar Nijar mai makwabataka da Libyar Briji Rafini, ya ce kawo yanzu manyan jami'ai na gwamnatin Kaddafi su 32 ne suka shiga a kasar ta Nijar cikinsu kuwa har da dansa mai suna Sa'adi Kaddafi.
859362