Bangaren kasa da kasa, an kai wasu munanan hare-hare kan ofisoshin jakadancin Amurka da ke biranan Kabul na kasa Afghanistan da kuma Tripoli na kasar Libya wanda wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne suka kaddamar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya naklato daga kamfanin dilalncn labaran REAUTERS cewa, a cikin makonan an kai wasu munanan hare-hare kan ofisoshin jakadancin Amurka da ke biranan Kabul na kasa Afghanistan da kuma Tripoli na kasar Libya wanda wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne suka kaddamar da nufin kara jefa Amurka cikin rashin kwanciyar hankali.
Wani rahoton kuma yana cewa karon farko tun bayan faduwar gwamnatin Gaddafi a kasar Libiya shugaban Majalisar Wucin Gadi da ke wakiltan masu bore a kasar Mustafa Abdul-Jalil ya shiga birnin Tripoli fadar mulkin kasar ta Libiya a jiya asabar.
Ministan harkokin cikin gidan kasar Libiya a Majalisar Wucin Gadin kasar Ahmad Dharad ya bayyana cewar zuwan Mustafa Abdul-Jalil cikin birnin Tripoli dalili ne da ke tabbatar da cewar mulkin kama karya na Mu'ammar Gaddafi ya kawo karshe a kasar Libiya.
Daruruwan jama'a ne suka tarbi shugaban Majalisar Wucin Gadin Mustafa Abdul-Jalil bayan isarsa birnin na Tripoli karkashin tsauraran matakan tsaro.
860323