IQNA

Rasha Na Goyon Bayan Kafa Kasar Palastinu Mai Cin Gishin Kanta

19:02 - September 14, 2011
Lambar Labari: 2187510
Bangaren kasa da kasa, kasar Rasha na goyon bayan kafa kasar Palastinu mai cin gishin kanta matukar dai a gabatar da wannan Magana a zaman abban zauren majalisar dinkin duniya a zaman da zai gudanar a nan gaba.

Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na atlasinfo cewa, kasar Rasha na goyon bayan kafa kasar Palastinu mai cin gishin kanta matukar dai a gabatar da wannan Magana a zaman abban zauren majalisar dinkin duniya a zaman da zai gudanar a nan gaba domin samun kafa kasa a gefen Isra'ila ta palastinawa.
Shugaban kasar Rasha Demtry Medved ya yi kakkausar suka ga irin matakan da kasashen Amurka da kawayenta suke dauka a kan kasar Syria sakamakon adawar da wasu mutane ke yi da gwamnatin Basharul Assad, yana mai cewa har gobe Rasha ba za ta goyi bayan kuduri mai neman a kakaba wa kasar takunkumi kamar dai yadda Amurkar da wasu kasashe na Turai suke bukata ba.
Medvedv wanda yake gabatar da taron manema labarai a birnin Moscou a wannan litinin.
Ya ce dole ne kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi wa gwamnati da al'ummar Syria adalci ta hanyar fitowa ya yi suka ga mutanen da suke kai wa jami'an tsaron kasar hari da makamai a maimakon zargin gwamnatin na cewa tana kasashe fararen hula.

Wannan furuci na shugaban Medveded ya zo ne a daidai lokacin da manzonsa na musamman a yankin gabas ta tsakiya Mikha'il Margelov yake ganawa da manzon shugaban Bashar Assad Buseyna Sha'aban a birnin Moscou. Kasar Rasha dai ce ta tsaya kai da fata wajen ganin cewa Amurka da kawayenta ba su samu nasara ba a kokarinsu na haddasa yaki ko kuma kifar da gwamnatin Assad ta hanyar fakewa da Majalisar Dinkin Duniya.
860161



captcha