Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na salon-monde-muslman cewa ana shirin fara gudanar da wani zaman taro mai taken manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi (SAW) a birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa da nufin kara bayyana addinin muslunci ga al’ummar, wadan suke da karancin fahimta kan addinin muslunci.
A cikin ayoyin da suka gabata mun ji irin yadda munafukai suke yi wa manzon Allah zagon kasa domin kawo masa matsala a cikin lamarinsa na tafiyar da al’umma bisa koyarwar addinin muslunci, haka nan ma wannan aya mai albarka tana yin bayani ne kan yadda wasu munafukai suke yada jitajita tsakanin muminai da nufin raunana imaninsu.
Musamman ma kan batun yaki, da lamurin tsaro, a lokaci guda kuma tana yi mana ishara da yadda ya zama wajibi a mayar da lamari ga wadanda su ne jagori na addini masu tsoron Allah da tsentseni da kuma sanin lamurra ta fuskar ilimi na addini, wadanda su ne za su iya warware matsaloli a cikin rayuwar zamantakewar musulmi.
Irin wannan tabi’a ta munafukai tana kai mutum zuwa ga kafirci da zama mabiyin shaidan, da ba don falalar Allah da jagorancin manzon Allah (SAW) ba, da mutane da yawa sun halaka ta hanayar bin shaidan, da sun rabu da tafarkin ubangij.
860097