Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya samu daga shafin yanar gizo an bayyana cewar, nan da ‘yan kwanaki za a gudanar da wani taron addinin musulunci na kusanto da mazjhabobin domin kara samun fahimtar juna da hadin kai tsakanin musulmi wanda zai gudana a birnin London wanda cibiyar kusantoo da mazhabobin musulunci za ta dauki nauyin gudanarwa.
Ya zo a cikin wasu ruwayoyin tarihi cewa, bayan da musulmi suka fuskanci matasala a yakin Uhud, dag abisani Abu Sufyan wanda a lokacin yana cikin manyan Mushrikan Kuraishawa, ya shirya wani makirci da nufin yaudarar manzon Allah da sauran musulmi, da nufin yin kwaf daya a kan muminai, amma Allah ya fadakar da manzonsa (SAW) makircin mushrikai.
kuma Allah ya kare manzonsa da sauran muminai da suke tare da shi mummunan kudirin Abu Sufyan da sauran Mushrikan Kuraishawa. Domin kuwa Abu Sufyan ya gayyaci manzo zuwa wani wuri ne inda yake ganin a lokacin rundunar mushrikai za ta iya gamaya da manzon Allah (SAW) kuma manzo ya je wurin amma mushrikai sun firgita sun kasa tunkarar ma’aiki (SAW)
Gudanar da wani taron addinin musulunci na kusanto da mazjhabobin domin kara samun fahimtar juna da hadin kai tsakanin musulmi wanda zai gudana a birnin London yana da matukar muhimmanci a wannan yanayi da ake bukatar hadin kai tsakanin musulmi.
860073