IQNA

Imam Khomeini (RA) da Jagoran Juyi Suna Girmama Sauran Ra'ayoyi

11:54 - September 15, 2011
Lambar Labari: 2187650
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin abubuwan da marigayi Imam Khomeini da kuma jagoran juyin juya halin muslunci na iran Ayatollah Ozma Sayyid ali khamenei suka kebanta da shi girmama sauran ra'ayoyi da addinai.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tsohon pira ministan kasar Iraki Dr. Ibrahim Jafari ya bayyana cewa daya daga cikin abubuwan da marigayi Imam Khomeini da kuma jagoran juyin juya halin muslunci na iran Ayatollah Ozma Sayyid ali khamenei suka kebanta da shi girmama sauran ra'ayoyi da addinai an duniya, wanda hakan shi ne kuma babban abin da ake bukata daga jagorori na hakika a duniya.

Dr. Ibrahim Jafari ya sheda hakan ne jiya alokacin da yake gabatar da jawabinsa a gaban taron kasa da kasa na babbar cibiyar Ahlul-Bait ta duniya da aka gudanar a birnin Tehran, inda ya kasance cikin wadanda suka wakilci kasar Iraki a wajen wannan taro.

Ya ce a halin yanzu jagoran juyin juya halin muslunci na kasar Iran Ayatollah Ozma Sayyid ali Khamenei shi ne wanda yake wakiltar irin wancan tunani da mahanga ta Imam Khomeini (RA) kuma wajibi ne dukkanin shugabannin muslumi su koyi da irin wannan mahanga matukar dai suna son a samu fahimtar juna tsakanin addinai.

Jafari ya kara da cewa daya daga cikin abubuwan da marigayi Imam Khomeini da kuma jagoran juyin juya halin muslunci na iran Ayatollah Ozma Sayyid ali khamenei suka kebanta da shi , hard a sanin zamaninda suke rayuwa a ciki, da yadda ya kamata musulmi ya kasance a cikin zaanin.

861090
captcha