IQNA

Mikewar Musulmi Sakamako Ne Na Masu Isar da Sakon Addini

17:03 - September 15, 2011
Lambar Labari: 2187781
Bangaren kasa da kasa, abubuwan da suke faruwa na sauyi a cikin kasashen musulmi musamman ma kasashen larabawa sakamako ne kokarin da musulmi suke yi wajen kara wayar da kan sauran mutane kan hakkokinsu kamar yadda adini ya ayyana su.


Kamfanin diallcnin labaran iqna ya habarta cewa ya samu wani labar daga shafin sadarwa na yanar gioz cewa abubuwan da suke faruwa na sauyi a cikin kasashen musulmi musamman ma kasashen larabawa sakamako ne kokarin da musulmi suke yi wajen kara wayar da kan sauran mutane kan hakkokinsu kamar yadda adini ya ayyana su kuam aka karanta su a cikin addinin muslunci.

ِA bangare guda kuma wasu rahotannin sun yi nuni da cewa daidai lokacin da zuriyar Ali Khalifa mai mulki a kasar Bahrain ta ke ci gaba da cutar da al'ummar kasar ta hanyar kame da kuma azabtarwa a gidajen kurkuku, mutanen kasar sun bude wani sabon salo na bore, masu son kawo sauyi a fagen siyasar kasar Bahrain sun bude wani shafi na boren da su ke yi ta hanyar yajin cin abinci da kuma yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su tseratar da wadanda ake tsare da su a gidajen kurkuku sannan kuma a haramta zaben da mahukuntan kasar su ke son gudanarwa.

Mutanen da su ke yin yajin cin abinci a cikin gidajen kurkuku da kuma waje, suna da yawan gaske. Likitocin da aka kama sannan aka tsare su a cikin gidan kurkuku ne su ka fara gudanar da yajin cin abinci. Halin da likitocin su ke ciki a kurkuku ya yi muni ta yadda babu mafita sai da aka fitar da su zuwa asibitoci daban-daban, daga cikin wadanda ake tsare da su da akwai babban lauyan nan Abdul-Hady Khaja wanda shi ma ya shiga cikin yajin cin abinci.

Da akwai kananan yara masu yawan gaske da su ka nuna goyon bayansu ga likitocin wanda su ma an kai su gidajen kurkuku, suma suna shiga cikin masu yajin cin abincin, shigar yaran cikin yajin cin abinci ya motsa mutane da dama na kasar Bahrain tare da gudanar da zanga-zangar kira da a saki dukkanin fursunonin da ake tsare da su.
Samarin da su ke jagorantar yunkurin 14 ga watan febrairu sun yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da na kare hakkin bil'adama da su tsoma baki domin sakin fursunonin siyasa da ake tsare da su.

Bugu da kari kungiyoyin siyasa na hamayya a kasar sun yi kira ga mutane da su kauracewa zaben da masu mulki su ka shirya wanda za a yi a cikin wannan watan na Satumba, saboda sun bayyana shi da cewa yaudara ce kadai a cikinsa.
860713

captcha