Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Mariv da ake bugawa a haramtacciyar kasar Isra'ila cewa, haramtacciyar kasar ta nuna matukar damuwa dangane da makomar ofishinta da ke birnin Amman na kasar Jordan bayan da al'ummar kasar suka bukaci da a kori jakadan yahudawan sahyunoiya daga kasarsu, wanda suke ganin cewa shi ne tushen dukaknin matsaloli.
Bayanin ya ci gaba da cewa Rahotanni daban-daban da suke fitowa daga kasar Siriya suna nuni da hannun kasar Saudiyya dumu-dumu cikin tashin tashinan da a halin yanzu yake faruwa a kasar Siriyar da nufin kifar da gwamnatin kasar da kafa wata gwamnati ta 'yan amshin shatan kasashen yammaci mai mika wuya ga.
Kamfanin dillancin labaran kasar Siriyan ya nakalto daya daga cikin 'yan ta'addan da aka kama a garin Hama na kasar Siriyan a lokacin da yake kokarin kai hare-hare a garin yana bayyana irin hannun da 'yan kungiyar salafiyyan nan ta 'Jundush Sham' da kuma wasu 'yan kasar Saudiyya suke da shi cikin rikicin baya-bayan nan da ke gudana a halin yanzu a kasar Siriyan.
Shi dai wannan mutumin mai suna Ammar Ziyad wanda gidan talabijin din kasar Siriya ya watsa bayanan da ya yi a lokacin da ake gudanar da bincike kansa ya bayyana cewar wadannan mutanen dai sun shigo garin na Hama ne daga waje dauke da muggan makamai sannan kuma babban abin da suka sa a gaba shi ne kai hare-hare cibiyoyin soji da na 'yan sanda.
Kungiyar Jundush Sham dai wata kungiya ce ta 'yan salafiyya wadanda mafiya yawansu suna zaune ne a sansanin 'yan gudun hijiran Palastinawa da ke kudancin kasar Labanon. A shekara ta 2009 ma dai 'yan wadannan kungiyar sun kai hari kan wata cibiyar tsaro ta kasar Siriyan inda suka kashe mutane 17.
Har ila yau a ci gaba da bayanin da ya ke yi, wannan dan ta'addan da aka kaman ya yi ishara da yadda aka ba su kudade don kirkiro labaran karya da hotuna na boge da aika su zuwa ga tashoshin talabijin din Al-Jazeera mallakar kasar da kuma Al-Arabiyya mallakan kasar Saudiyya da nufin tuhumar sojojin kasar Siriya kan cewa su ne suke kashe mutane masu zanga-zanga a kasar, duk dai da nufin bakanta sunan kasar Siriya a idon duniya.
860707