Bangaren kasa da kasa, mafi yawan mutanen kasar Masar suna goyon bayan a hukunta tsohon shugaban mukin kama karya na kasar a gaban kotu kan manyan laifukan da ya tafka a lokacin yan akan karagar mulkin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar Ahram ta masar cewa mafi yawan mutanen kasar Masar din, suna goyon bayan a hukunta tsohon shugaban mukin kama karya na kasar a gaban kotu kan manyan laifukan da ya tafka a lokacin yan akan karagar mulkin kasar wanda ya kwashe shekaru talatin da biyu.
Abin da yake a fili shi ne cewa kasashen yammaci da 'yan amshin shatansu na kasashen larabawa sun daura damarar fada da gwamnatin Siriya ta hanyoyi daban-daban musamman ta bangaren kafafen watsa labarai da nufin kawo karshenta, kamar yadda a halin yanzu a ke ganin hakan a fili ta yadda irin wadannan kafafen watsa labarai musamman na larabawa suka matsa kaimi kan Siriya da rufe ido kan irin danyen aikin da masu dauke da makami na kasar suke yi ciki kuwa har da zubar da jinin fararen hula da jami'an tsaron kasar.
To sai dai kuma har ya zuwa yanzu dai makiyan Siriya sun gagara cimma wannan manufa ta su sakamakon irin taka tsantsan din da al'ummar Siriyan suka nuna da kuma irin aniyar da gwamnatin kasar ta dauka na haifar da sauye-sauye a kasar don biyan bukatun al'ummar kasar.
860654