Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar kasar Masar ta Yaum Al-sabi cewa, tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Tunisia Zainul Abidin Bin Ali a gaban kotun soji ta kasar, zai fuskanci hukunci tare da wasu na hanun damarsa da suka tafka laifukan kisa gilla a kan mutane masu gudanar da zanga-zangar neman sauyi da canji na siyasa.
Wani rahoton da hukumar kidayar jama'a ta kasar Amurka ta fitar na nuni da cewa kasar na fuskanci mafi munin yanayin talauci cikin sama da shekaru ashirin din da suka gabata inda kashi 15.1 na Amurkawan suke rayuwa kasa da mizanin talauci.
A cikin kididdigar da hukumar kidayar jama'ar ta Amurka ta fitar a jiya talata, ta bayyana cewar kimanin Amurkawa miliyan 46.2 suna cikin matsanancin talauci wanda hakan shi ne adadi mafi yawa tun da hukumar ta fara fitar da irin wannan kididdigar kimanin shekaru 52 da suka gabata.
Wannan kididdigar dai tana nuni ne da irin mawuyacin yanayin tattalin arziki da Amurkan take ciki cikin 'yan shekarun nan inda a halin yanzu akwai sama da mutane miliyan 14 da ba su da aikin yi a kasar Amurkan, lamarin da ke kara irin nuna rashin amincewar da al'ummar kasar suke yi ga tsarin mulkin kasar.
861739