Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto rahot daga gidan talabijin din Almanar na kasar Lebanon cewa kungiyar Ikhwanul muslimin ta kasar Masar ta yi kakkausar suka kan matsayin da pira ministan kasar Turkiya Rajab Tayyib Ardugan ya dauka na neman ya zama shugaban musulmi da larabawa baki daya, musamman ma bayan farin jinin da Turkiya ta samu bayan kasha 'yan kasarta da za su kai dauki ga al'ummar Gaza.
Wani rahoton kuma ya ce, jakadan kasar Siriya a kungiyar hadin kan kasashen Larabawa Yusuf Ahmad ya yi watsi da sanarwar bayan taron ministocin kasashen larabawa da suka fitar a jiya talata bayan taron da suka gudanar a helkwatar kungiyar da ke birnin Alkahira na kasar Masar.
Wakilin kasar Siriyan ya bayyana wannan sanarwar a matsayin alamar adawa da kasar Siriya sannan kuma wani kokari na yin kafar ungulu ga kokarin da babban sakataren kungiyar ya faro wajen magance matsalar da ta kunno kai a kasar Siriyan.
Jakada Yusuf Ahmad ya kara da cewa tun farko wasu gwamnatocin kasashen larabawan da kafafen watsa labaransu sun ta kokarin wajen ganin wannan kokarin bai yi nasara ba, yana mai tuhumarsu da gudanar da abubuwan da manyan kasashen duniya suke son gudanarwa a kokarin da suke yi na kulla wa kasar Siriyan makirci da kifar da gwamnatin kasar.
Daga karshe dai jakadan kasar Siriya ya ce gwamnatin kasar za ta ci gaba da gudanar da shirin sauyi da ta kaddamar a kasar ba tare da la'akari da irin wadannan makirce-makircen da ake kulla mata ba.
861687