Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, daya daga cikin fitattun 'yan siyasa a saudiyya ya bukaci kafa wata doka da za ta hana kafirta sauran musulmi a kasar saudiyya duk kuwa da cewa babu wani mai suna demokradiya da ake bi a kasar amma hana kafirta musulmi zai sanya birki ga masu tsatsauran ra'ayin wahabianci da kuma akidar nan ta salafiyanci.
Rahotanni daban-daban da suke fitowa daga kasar Siriya suna nuni da hannun kasar Saudiyya dumu-dumu cikin tashin tashinan da a halin yanzu yake faruwa a kasar Siriyar da nufin kifar da gwamnatin kasar da kafa wata gwamnati ta 'yan amshin shatan kasashen yammaci mai mika wuya ga
Kamfanin dillancin labaran kasar Siriyan ya nakalto daya daga cikin 'yan ta'addan da aka kama a garin Hama na kasar Siriyan a lokacin da yake kokarin kai hare-hare a garin yana bayyana irin hannun da 'yan kungiyar salafiyyan nan ta 'Jundush Sham' da kuma wasu 'yan kasar Saudiyya suke da shi cikin rikicin baya-bayan nan da ke gudana a halin yanzu a kasar Siriyan.
Shi dai wannan mutumin mai suna Ammar Ziyad wanda gidan talabijin din kasar Siriya ya watsa bayanan da ya yi a lokacin da ake gudanar da bincike kansa ya bayyana cewar wadannan mutanen dai sun shigo garin na Hama ne daga waje dauke da muggan makamai sannan kuma babban abin da suka sa a gaba shi ne kai hare-hare cibiyoyin soji da na 'yan sanda.
Kungiyar Jundush Sham dai wata kungiya ce ta 'yan salafiyya wadanda mafiya yawansu suna zaune ne a sansanin 'yan gudun hijiran Palastinawa da ke kudancin kasar Labanon. A shekara ta 2009 ma dai 'yan wadannan kungiyar sun kai hari kan wata cibiyar tsaro ta kasar Siriyan inda suka kashe mutane 17.
Har ila yau a ci gaba da bayanin da ya ke yi, wannan dan ta'addan da aka kaman ya yi ishara da yadda aka ba su kudade don kirkiro labaran karya da hotuna na boge da aika su zuwa ga tashoshin talabijin din Al-Jazeera mallakar kasar Qatar da kuma Al-Arabiyya mallakan kasar Saudiyya da nufin tuhumar sojojin kasar Siriya kan cewa su ne suke kashe mutane masu zanga-zanga a kasar, duk dai da nufin bakanta sunan kasar Siriya a idon duniya.
861700