IQNA

Yarjejeniyar Camp David Da Yahudawa Sahyuniya Ba Abu Ne Mai Tsarki Ba

17:37 - September 17, 2011
Lambar Labari: 2188702
Bangaren kasa da kasa, yarjejeniyar da aka kula tsakanin wasu daga cikin shgabannin larabawa da kuma yahudawan sahyuniya da aka sani da camp David ba wani abu ne da aka safkar daga sama ba.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto rahoto daga shafin sadarwa na jaridar Al-bilad da ake bugawa a kasa Algeria cewa, pira ministan kasar Masar Isam sharaf ya bayyana cewa yarjejeniyar da aka kula tsakanin wasu daga cikin shgabannin larabawa da kuma yahudawan sahyuniya da aka sani da camp David ba wani abu ne da aka safkar daga sama ba, saboda haka za aiya yin watsi da ita.

Wani rahoton kuma ya ce Jakadan Haramtacciyar Kasar Irsa'ila a kasar Masar Yitzak Levanon, a sanyin safiyar yau asabar ya gudu ya bar birnin Alkahira bayan da matasa masu zanga-zanga suka afka wa ofishin jakadancin wannan kasa maras halacci da ke birnin.

A jiya juma'a dubun dubatar mutane ne suka yi wa ofishin jakadancin na 'yan sahyuniyya kofar raga duk da cewa an jibge dimbin jami'an tsaro domin bai wa ofishin kariya. Masu zanga-zangar wadanda ke neman kasarsu ta Masar ta yanke huldar deplomasiyya da Isra'ila, sun yi artabu da 'yan sanda sanna kuma suka karya shingaye da aka kafa a zagayen ofishin jakadancin.

A sanyin safiyar yau asabar kuwa, ministan yaki na Ehud Barack ya tattauna da sabon sakataren tsaron Amurka Leon Panetta, inda ya bukaci Amurkar da ta taimaka domin bayar da kariya ga ofishin jakadancinsu da ke birnin Alkahira. Fiye da mutane milyan daya ne suka gudanar da zanga-zanga a jiya juma'a a birnin Alkahira kawai.

Inda suka bukaci majalisar mulkin sojan kasar da ta bayyana wa 'yan kasar ranakun da za'a gudanar da zabuka da kuma mayar da mulkin kasar a hannun zababbiyar gwamnatin demokradiyya bayan kawar da dan kama karya Husni Mubarak daga kan karagar mulki.

861667
captcha