Bangaren kasa da kasa, kwamitin da ke kula da harkokin masallacin Qods ya yi gargadi dangane da barazanar da yahudawan sahyuniya suke kan masallacin da makomarsa wanda hakan ke nufin shiga rikici tsaknains da musulmi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalt daga shafin sadarwa na yanar gizo na palastine Info cewa, kwamitin da ke kula da harkokin masallacin Qods ya yi gargadi dangane da barazanar da yahudawan sahyuniya suke kan masallacin da makomarsa wanda hakan ke nufin shiga rikici tsaknains da musulmi da ma mabiya wasu addinan kamar kiristoci da kuma yahudawa masu son zama lafiya.
A bangare guda kuma Wani mutumin da ya yi wa aikin leken asiri ya yi ikirarin cewa yana da hannu a kisan gillan da aka yi wa babban kwamandan kungiyar Hizbullah Imad Mughniyah a shekarar 2008 a birnin Damascus na kasar Siriya,gidan talbijin na gwamnatin Siriya ya sanar a jiya Asabar cewa wani bapalasdine mazaunin kasar Jordan ya ce ya bada bayanan sirri wa jamian hukumar leken asirin Israila dangane da wasu wurare a cikin kasar Siriya.
Hakazalika mutumin ya ce ya taimaka wajen kisan gillan da aka yi wa Imad Mughniyah wanda wani bam ya sanadiyar shahadarsa a birnin Damascus a shekarar 2008, tun bayan shahadar Imad Mughniyah, gwamnatin kasar Siriya ta zargi Israila da aikata wannan taaddanci amma gwamnatin Sahyoniya ta musanta zargin.
862042