Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na AFP cewa daruruwan masu adawa a kasar Kuwait suka bukaci da a kafa gwamnatin da mutane za su zaba da kansu a matsayin wani mataki na neman gyara a cikin harkokin mulki da siyasar kasar wadda day ace daga cikin kasashen larabawa da suke mulki na mulukiya.
Kamar yadda mu ka ambata, musulunci yana yin kira zuwa ga samar da daidaito acikin al’ummar musulmi wanda ciyarwa tana daga cikinsu. Wato masu wadata da wadanda su ke da dama su taimakawa da mabukata da dukiyar da su ke da ita.
Wannan ayar tana yin ishara ne akan wani yanayi mai muhimmanci wanda ya shafi muhajirun da masu jihadi, wadanda su ka zama ‘yan gudun hijira bayan sun baro gidajensu, suna rayuwa acikin bakunta ba tare da kudi ba kuma basu da damar yin kasuwanci, sai dai duk da wannan irin halin da su ke ciki sun kame kai ba su yin bara, kuma basu bayyana bukatunsu a fili.
Saboda haka dukkanin mutane su ke daukar cewa su mawadata ne, alhali wajibi ne ga dukkanin muminai su zama masu yin tunani akan yadda za su kare mutuncin ‘yan’uwansu na addini kada su barsu cikin wahala.
862115